We provide Sheikh Aminu Daurawa - Sirrin Zaman Aure Mp3 online (apkid: com.andromo.dev658544.app668550) in order to run this application in our online Android emulator.


Description:

Run this app named Sheikh Aminu Daurawa - Sirrin Zaman Aure Mp3 using MyAndroid.
You can do it using our Android online emulator.

The app requires no internet connection to work (it is Offline) and voice quality is very high.
Just download and start listening even when offline.
-------
Wannan app yana dauke da wasu zababun lekcoci masu taken " Sirrin Zaman Aure" daga Sheikh aminu ibrahim daurawa ke gabatarwa, wanda yake fadakarwa da kuma bada shawarori akan yadda Miji da Mata zasu zauna cikin aurensu lafiya, shine muka ga ya dace muyi application wanda mutane zasu su saurara a saukake.
Allah ya sakawa Sheikh ibrahim aminu daurawa domin yayi kokari wajen yayi kokari wajen yada ilimin Allah da na manzon sa domin karuwar al'umar musulmai.
Mukuma Allah ya bamu ikon ji da kuma amfani daga abin da muka saurara.
Bayan bayani akan Sirrin Zaman Aur, akwai lectures na Sheikh ibrahim aminu daurawa da kuma karatuttuka a cikin wannan manhaja idan akayi duba.
Akwai karatun malam Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 akan illar harshe, matsalolin aure by Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 dai sauransu.
za kuma a iya samun wasu karatuttukan na wasu malam irin su sheikh jafar mahmud adam, sheikh albani zariya, sheikh ali isah fantami, shiekh kabir gombe.
Za kuma a iya samun Karatun Al-quran na wasu daga cikin manyan makaranta quran.
Don Allah idan har kaji dadin wannan application a taimaka a yi sharing ta facebook, whatsapp, twitter, instagram da sauran social media domin sauran yan uwa musulmi su ma suyi downloading su amfana.
Kada kuma a manta ayi rating na wannnan application five star.
Kadan daga cikin tarihin Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa,
TARIHIN SHEIKH AMINU DAURAWA KANO : -
Sunana Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal.
Mahaifina shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Fagge.
Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da tsohuwar tashar kuka.
Tsawon shekaru arbain, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,
bayan kasuwanci da sanaar dinki, domin dogaro da kai.
Sunan mahaifiyata Hajiya Saadatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32 unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala.
Na fara karatun Alqurani mai girma tun ina dan karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15.
Bayan firamare da sakandare, da na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqurani da tafsir, wasu na Alqurani zalla, wasu na ilimi da fannoninsa daban-daban.
Wadannan manyan malamai su ne:
1.
Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqurani a wajensa.
2.
Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqurani a wajensa.
3.
Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqurani a wajensa.
4.
Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.
5.
Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.
6.
Sheikh Auwal Isa Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.
7.
Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a wajensa.
8.
Sheikh Idi Kajjin Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.
9.
Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.
10.
Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.
11.
Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a wajensa.
Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa.
Allah ya ji qansa da rahama!
12.
Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa.
Wannan malami, a wajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shuaraul Jahiliyya.
Malami ne mai haquri da juriyar karantarwa.
da dai sauran malamai daban daban a duniya.
Bayan wannan app mai suna Sirrin Zaman Aure, za iya samun wasu karatuttukan da sauran apps namu na wasu daga cikin manya-manya malamai, idan aka yi searchin (rrnapps) a play store.

MyAndroid is not a downloader online for Sheikh Aminu Daurawa - Sirrin Zaman Aure Mp3. It only allows to test online Sheikh Aminu Daurawa - Sirrin Zaman Aure Mp3 with apkid com.andromo.dev658544.app668550. MyAndroid provides the official Google Play Store to run Sheikh Aminu Daurawa - Sirrin Zaman Aure Mp3 online.

Page navigation:

©2025. MyAndroid. All Rights Reserved.

By OffiDocs Group OU – Registry code: 1609791 -VAT number: EE102345621.